A yau Litinin 2 ga wata, gwamantin kasar Thailand ta ce, tana nan a kan bakanta na cewa, hanyar zaman lafiya ne kadai za'a bi domin warware rikicin siyasa da ake fuskanta, in ji mukaddashin firaministan Surapong Towichukchaikul.
A taron manema labarai, Mr. Surapong ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati da su koma bakin aikinsu, duk da kiran da jagoran zanga-zanga wato Suthep Thaugsuban ya yi a ranar Lahadi cewa, a dakatar da aiki gaba daya a fadin kasar.
Surapong dai shi ne aka tsayar ya maye gurbin mataimakin firaminista Pracha Promnok, ya kuma tafiyar da sashin mulki da zamn lafiya da doka, kamar yadda aka sanar lokacin taron manema labaran.
An dauki lokaci mai tsawo, ana gudanar da zanga-zanga a kan tituna, abin da ya kawo illa ga tattalin arzikin kasa, ya kuma bata sunan kasar ta Thailand a idon duniya, in ji Mr. Surapong wanda har ila yau shi ne ministan harkokin wajen kasar.
Ya ce, gwamnati tana mutunta 'yancin al'umma wajen mika bukatunsu, amma ba daidai ba ne ga masu zanga-zanga su shiga cikin gine-ginen gwamnati su hana a tafiyar da aiki. (Fatimah)