Mr. Wang ya bayyana haka ne a yayin taron kara wa juna sani da kwamitin tsaron MDD ya kira kan batun tsaro, zaman lafiya da mata. Ya ce, a halin yanzu, mata su ne wadanda suka fi fama da barazana cikin rikice-rikice da dama da suka auku cikin duniya.
Bugu da kari, Mr. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta goyi bayan kwamitin tsaron MDD wajen gudanar da kudurin da abin ya shafa bisa dukkan fannoni, don yaki da hare-hare, musammman ma da ake kai wa fararen hula, ciki hada da hare-haren da suka shafi batun jinsi, ya kamata a bukaci bangarorin daban daban da rikice-rikicen suka shafa da su bi dokokin jin kai na kasa da kasa da wasu dokokin kasa da kasa da abin ya shafa, domin dakatar da munanan ayyukan dake shafar harkar jinsi tun da wuri, tare da daukar matakan kiyaye hakkin mata, yara da dai sauran mutane masu karamin karfi yadda ya kamata. (Maryam)