A yammacin ranar 23 ga wata, manzon MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta AL dangane da rikicin kasar Syria Lakhdar Brahimi ya gana da shugaban babbar kungiyar adawa ta kasar Ahmad Jarba da mataimakin firaministan kasar kuma ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Muallem daya bayan daya, don ba da tabbaci game da abubuwan da za a tattauna a shawarwarin.
An ce, ba za a yi shawarwari ido da ido ba a tsakanin tawagar gwamnatin Syria da bangaren adawa. Bayan bikin bude mataki na biyu na taron, sassan biyu za su zauna a wurare daban daban, inda Lakhdar Brahimi zai saurari bayyanan ko wanen bangare. Akwai sharhin dake cewa, ko da yake a matakin farko na shawarwarin, sassan biyu sun yi muhawara mai tsanani kan ko shugaba Bashar al-Assad zai ci gaba da zama kan mukaminsa ko a'a, amma duk da haka, an samu mafari mai kyau, saboda sassan biyu har yanzu na kan teburin shawarwari.
Tashe-tashen hankulan da suka faru a kasar Syria sun jawo hankulan kasashen duniya sosai. Shugaban kasar Lebanon, Michel Suleiman a ranar 23 ga wata a birnin Beirut ya bayyana cewa, kasarsa na fatan za a samu nasara a taron Geneva karo na biyu kan batun Syria da har yanzu ake gudanarwa. Ya kuma yi kira ga sassa daban daban na kasar Lebanon da su dauki matakan da suka dace, ta yadda za a cimma ra'ayi daya tsakanin sassa daban daban na kasar ta Syria, domin warware rikicin da ake fama da shi a kasar a siyasance, tare kuma da taimaka wa 'yan gudun hijira na kasar don su koma kasarsu cikin hanzari.
A nasa bangaren, shugaban kasar Iran, Hassan Rohani ya yi bayani a wannan rana a dandalin tattalin arziki na Davos cewa, "shirya zabe cikin 'yanci da adalci ita ce hanyar da za ta taimaka wajen kawo karshen yakin basasa na kasar Syria", yana ganin cewa, kamata ya yi a bar jama'ar Syria su tabbatar da makomar kasarsu, a sa'i guda ya yi gargadi ga kasashen yammacin duniya cewa, kada su tilasta wa kasar Syria amince da shirinsu na warware rikicin kasar. (Bilkisu)