Cimma burin bunkasuwa na kashi 7 cikin 100 da aka tsaida a wannan shekara ba abu ba ne mai sauki, dalilin cewa irin wannan karuwa na nufin ya kai daidai da girman tattalin arziki madaidaici, a cewar faraminista Li Keqiang a yayin wani taron manema labarai da aka shirya a bayan taron NPC shekara-shekara.
Tattalin arzikin kasar Sin zai yi aiki bisa wani misalin da ya dace, a yayin da ci gaban tattalin arziki ke shiga wani sabon yanayin daidaituwa.
GDP kasar Sin ya karu da kashi 7.4 cikin 100 a shekarar 2014, kwatankwacin karuwarsa mafi karanci tun a shekarar 1990.
Albishir shi ne ba a yi amfani ba da wasu mayan tsare tsare na habakawa a wadannan shekaru biyu na baya bayan ba domin bunkasa ci gaban tattalin arziki. Wannan na ba mu damar samun wata babbar dama ta yin aiki ta fuskar siyasar tattalin arziki, kuma har yanzu mu nada jerin matakan siyaya, in ji shugaban gwamnatin kasar Sin. (Maman Ada)