Yace jawabin da firaministan kasar Li Keqiang ya yi ya jaddada tsarin raya kasa a fannoni hudu a cikin rahoton aikin gwamnati, wato raya zaman al'umma mai annashuwa da jituwa daga dukkan fannoni, da zurfafa yin kwaskwarima a duk fannoni, da sa kaimin gudanar da harkokin kasa bisa doka, da kulawa da harkokin JKS yadda ya kamata.
A cewar shi wannan ba ma kawai ya bayyana niyyar da gwamnatin kasar ta dauka ta yin gyare-gyare ba, har ma ya bayyana yadda gwamnatin kasar take kulawa da rayuwar jama'a, da kuma kwarin gwiwarta ta kyautata rayuwar jama'a.
Haka kuma jakada Dosso ya karfafa cewa, kasar kwaddibuwa ba ta samu ci gaba sosai ba, saboda haka, kasar za ta sami darussa da dama a fannonin rage gibin dake tsakanin masu kudi da matalauta, da kyautata rayuwar jama'a da sauransu ta hanyar samun fahimtar wannan sabon tsarin a fannoni hudu.(Fatima)