Mista Li ya yi wannan furuci ne yayin taron manema labarai da aka shirya bayan kammala taron wakilan jam'ar kasar Sin na shekara shekara, wato babbar hukumar zartas da dokokin kasa.
Inda ya nuna cewa wasu ma'aikata sun saukaka hanyoyin tafiyar da hukumomin kasa, har ma wasu ba su nuna wata halayya maras kyau ba. Sannan Mr. Li ya jaddada cewa, ba a yarda da ma'aikatan gwamnati su yi kasala kan ayyukansu ba.
Baya ga haka kuma Li keqiang ya jaddada muhimmancin kasa mai 'yanci wajen yaki da cin hanci, tare da bayyana cewa babu mutumin da aka baiwa umurnin gudanar da aiki a bayan wanda tsarin doka ya tanada. Faraminista Li Keqiang ya bayyana cewa ya kamata ma'aikata su karfafa tunanisu na da'a, ta amfani da ikonsu domin jin dadin al'ummar kasa maimakon dukufa ga neman moriyarsu kansu. (Maman Ada)