An kammala taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 12 a yammacin yau Juma'a 13 ga wata.
Manyan shugabannin kasar ciki hadda Xi Jinping, Li Keqiang, Zhang Dejiang, Yu Zhengsheng, Liu Yunshan, Wang Qishan, Zhang Gaoli da kuma 'yan majalisar 2,114 suka halarci bikin rufe taron karkashin jagorancin Mr Yu Zhengsheng, shugaban majalisar.
A kudurin da aka fitar a wajen taron an bayyana cewa wannan shekara da ake ciki shekara ce mai muhimmanci wajen zurfafa yin kwaskwarima, kuma shekara ce da aka fara aiwatar da manufar gudanar da harkokin kasa bisa doka a dukkanin fannoni, har ma shekara ta karshe wajen gudanar da shirin shekaru biyar-biyar na 12 na raya kasar Sin. Kuduri kuma ya nuna cewa, ya kamata majalisar ta yi nazari sosai kan wasu manyan batutuwa musamman ma ba da shawara kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda tsai da shirin shekaru biyar-biyar karo na 13 na raya kasar, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin karko, sannan kuma da yada muhimmin tunani mai tushe na gurguzu da dai sauransu.
Ban da haka kuma, bikin rufewa taron ya zartas da kuduri game da rahoton ayyukan kwamitin gudanarwa na majalisar ba da shawara da rahoton dangane da aikin nazarin shawarwarin da aka gabatar.
Rahoton dangane da aikin nazarin shawarwarin da aka gabatar ya nuna cewa, ya zuwa karfe 2 da yamma a ran 7 ga watan, yawan shawarwarin da aka gabatar a wannan karo ya kai 5857, an kebe su zuwa kaso 14, ciki hadda batutuwan dake dangane da raya tattalin arziki, siyasa da dokoki da shari'a, zaman al'umma, kimiya da fasaha, ba da ilmi, yada al'adu, aikin jiyya da motsa jiki, makamashi da muhalli da sauransu. (Amina)