in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rono ta lashe gasar gudun yada kanin wani ta kasar Kenya
2015-03-12 14:41:45 cri
Matashiyar 'yar wasan tseren kasar Kenya Georgina Rono, ta samu nasarar lashe gasar tseren yada kanin wani da aka gudanar a birnin Nairobin kasar Kenya, gasar da aka shirya a gabar da ake gudanar da bikin ranar mata ta duniya.

Rono 'yar shekaru 35 a duniya, ta gama gudun ta cikin sa'a 1 da minti 4 da kuma dakika 5, yayin da wadda take biye mata Mercy Kibarus ta kammala na ta gudun cikin sa'a 1 da mintuna 8 da kuma dakika13.

Sai kuma ta uku Caroline Kilel, wadda ta taba lashe gasar tseren yada kanin wani ta birnin Boston, a wannan lokaci ta gama na ta gudu ne cikin sa'a 1 da mintuna 8 da kuma dakikoki 23, ya yin da Mercy Chemutai ta kasance ta hudu.

Rono ta shaidawa manema labaru cewa ba abu ne mai sauki lashe wannan gasa a Kenya ba, saboda tarin kwararrun 'yan tsere dake kasar. Ta kuma bayyana farin cikin ta da wannan nasara da ta samu.

A daya bangaren kuma tsohuwar zakarar gasar Olympic ta gudun mita 3,000 ajin matasa mata Gladys Chesir, ta samu nasarar lashe gasar tseren kilomita 10 cikin mintuna 30 da dakikoki 35, yayin da abokiyar tseren ta Anne Wanjiru, ta zamo ta biyu bayan da ta gama na ta gudun cikin mintuna 30 da dakikoki 40.

A ajin maza kuwa Moses Kosgei, ya doke Abel Kirui, mutumin dake rike da kambin gasar tseren yada-kanin wani ta duniya har karo biyu, da kuma Mathew Kisorio wanda ya taba zamowa na 8, a gasar tseren yada-kanin wani ta birnin New York.

Rahotanni sun bayyana cewa Moses Kosgei ya lashe tseren da ya gudana a ranar Lahadin karshen mako ne, bayan ya kammala gudu cikin sa'a daya da minti 1 da kuma dakika 28.

Matar shugaban kasar Kenya Margaret Kenyatta ce ta shirya wannan gasa ta tsere, gasar da ake fatan za a yi amfani da ita, wajen tara kudaden da za a yi amfani da su a wani kamfe mai lakabin "The Beyond Zero Campaign", na rage mace-macen kananan yara yayin haihuwa a dukkanin fadin kasar ta Kenya.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakin sa William Ruto, na cikin dubban 'yan kasar da suka ganewa idanun su yadda wannan gasa ta wakana. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China