Zhou ya yi wannan tabbaci ne a wani taron manema labarai a ci gaba da ake yi a babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar na shekara shekara.
Gwamnan babban bankin yace a yadda saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu, tattalin arzikin kasar ya shiga wani sabon yanayi amma hakan ba ya nufin tattalin arziki kasar na cikin wani yanayi mai matsala ba, haka kuma tsarin kudade na kasar ba zai canza salo ba.
Ma'aunin tattalin arzikin kasar GDP ya na nuna karuwar shi da kashi 7.4 a cikin 100 a bara, adadin da ya fi kankanta tun a shekarar ta 1990, kuma ana sa ran a wannan shekarar ta 2015 zai kai ga kashi 7 ciki 100.( Fatimah Jibril)