Rahotanni daga kasar Saliyo na cewa dakin gwaje-gwajen kimiyya na sada zumunta tsakanin Sin da kasar ta Saliyo, ya fara gudanar da aikin bincike kan nau'oin kwayoyin cutar Ebola a hukunce tun daga ranar Larabar da ta gabata.
A ranar farko, bayanai sun nuna cewa kwararru dake aiki a dakin gwajin sun gudanar da bincike kan samfurin kwayoyin cutar guda 24, da suka hada da samfurin jini 12, da na kwayoyin cuta 12 wadanda aka dauko daga makogwaron mutane.
Bayan gudanar da bincike game da zazzabin cizon sauro da kuma cutar ta Ebola, an gano wani samfur dake dauke da cutar Ebola, da kuma wani dake dauke da cutar zazzabin cizon sauro.
A matsayin dakin gwaji daya tilo da ya dace da ma'aunin kungiyar kiwon lafiya ta duniya a kasar ta Saliyo, wannan dakin gwaji na sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Saliyo, na da na'urori mafiya inganci, inda ake iya gudanar da bincike kan samfurin Ebola har 200 a kowace rana.
Na'urorin zamani da ake bukata domin gudanar da aikin nazari da bincike dake wannan dakin gwaji, sun sanya shi zamo wa muhimmin sansanin bincike kan cutar Ebola, tare da aikin hana yaduwar kwayoyin cutar a kasar.(Lami)




