in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liberiya ta bude kan iyakarta da Saliyo
2015-02-25 14:07:32 cri

Kasar Liberiya ta sake bude kan iyakarta a ranar Lahadi, bayan matakin da shugabar kasar Ellen Johnson-Sirleaf ta dauka na ba da umurnin janye dokar ta bace a fadin kasar dalilin annobar Ebola. Gwamnatin Saliyo ita ma ta sake bude kan iyakarta da Liberiya.

Bayanai sun tabbatar da cewa, gwamnatin Saliyo ta aike da jami'ai domin ba da damar sake bude kan iyakar, in ji babban jami'in yankin Grand Cape Mount dake Liberiya, mista Mohamed Passewee a gaban 'yan jarida a ranar Talata.

Sake bude iyakokin ya samu babban tarbo daga al'ummomin kasashen biyu dake raba al'adu da tarihi iri daya, in ji mista Passewee.

Mun samu horo a ranar jiya ga dukkan mutanenmu dake kan iyaka domin su tabbatar da cewa, an kiyaye matakan rigakafi a yayin da mutane za su fara shige da fice daga ko wane bangare, in ji Mohamed Passewee.

Haka kuma, hanyoyin shige da fice na yankin Maryland zuwa kasar Cote d'Ivoire daga kudu maso gabashin Liberiya, an sake bude su tun cikin watan Febrairu, a cewar jami'an magireshin da aka ture wurin da suka tabbatar da cewa, kome ya daidaita kan shige da fice. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China