in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta jinjinawa IMF bisa yafewa Saliyo bashi
2015-03-10 10:31:27 cri

Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yabawa asusun ba da lamuni na IMF, bisa amincewar da ya yi na yafewa kasar Saliyo wasu basussuka.

Wata sanarwa da ofishin mataimakin daraktan yada labarai na hukumar gudanarwar AUn ya fitar, ta rawaito Zuma na cewa, yafe bashin, ya zo daidai gabar da tattalin arzikin kasar ta Saliyo ke cikin wani mawuyacin hali, sakamakon bullar cutar Ebola a kasar.

Zuma ta ce, cutar Ebola ta yi matukar barna a kasashen Saliyo, da Guinea da kuma Liberia. Don haka akwai matukar bukatar fara tunanin matakan da suka wajaba, na sake ginin wadannan kasashe bayan cimma nasarar dakile cutar.

Darajar tallafin bashin da IMF din ya yafewa Saliyo dai zai kai dalar Amurka miliyan 114.63, matakin da ake fatan zai yi matukar tallafawa Saliyon, wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki, da na hauhawar farashi, tare da gibin kasafin kudin shekarar nan ta 2015 da kasar ke fuskanta a yanzu haka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China