in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shandong Luneng dake mai da hankali kan horar da matasa
2014-12-24 10:31:40 cri

Yanzu bari mu karkata ga kasar Sin, inda za mu mai da hankali kan wani kulob din wasan kwallon kafa mai suna Shandong Luneng, wanda ya shahara wajen horar da matasan 'yan kwallo.

Shi dai wannan Kulob dake jihar Shandong a nan kasar Sin, ya kafa makarantar musamman ce ta horar da matasa fasahar taka leda shekaru 15 da suka wuce. Kuma tun bayan kafuwarta, daliban makarantar sun sha kasancewa zakaru a wasanni 56 na matakai daban daban, gami da lashe lambobin zinariya a manyan gasannin da ake shiryawa a nan kasar Sin, a karo na 10 da na 11, a wasannin ajin matasa.

Bisa wannan sakamako ne kuma za a iya ganin fasahar makarantar kulob din na Shandong Luneng a zahiri, a fannin horar da matasan 'yan kwallo. Duk da wannan sakamako da wannan makaranta ta samu a baya, a bara dukkanin kungiyoyin kwallon kafar matasa 'yan kasa da shekaru 20 da 'yan kasa da shekaru 18 na jihar ta Shandong, wadanda yawancinsu suka fito daga kulob din Luneng, ba su samu wata nasara ta azo a gani ba, a gasar wasannin kasar Sin karo na 12.

Hakan ya sa wasu ke hasashen ko dai manufar kulob din ta Luneng ta daina amfani ne? to, sai dai fa wani abu da aka kasa lura da shi a nan shi ne, cikin kulaf din matasa ta kasar Sin, akwai 'yan wasa 7 da suka taba samun horo a kulob din na Luneng, yayin da kungiyar Olympics ta kasar Sin ita ma ke da 'yan wasa 7 daga kulaf din na Luneng.

Wanda hakan ke shaida cewa kulob din ya canza manufarsa, wato maimakon dora matukar muhimmanci kan lashe wasanni daban daban, yanzu haka ya fara mai da hankali sosai kan horar da fitattun 'yan wasa matasa.

A cewar wani jami'in makarantar kulob din na Luneng, a da kulof din ya mai da hankali ne sosai kan kokarin samun nasarori a wasannin da suke gudana a kasar Sin, wanda hakan ya sanya kulob din lashe lambobin yabo masu yawa, amma yanzu kungiyoyi daban daban sun fara nuna ra'ayin rikau, da kokarin kare kai a gasanni, don tabbatar da samun nasara, don haka sakamakon wasannin da ake gani a yanzu, ba shi da alaka sosai da kwarewar 'yan wasa. Kuma wannan dalili ne ya sa kulob din na Luneng yin fatali da sakamakon wasanni, yake kuma baiwa horas da matasa matukar muhimmanci, ta yadda za a kai ga samun fitattun 'yan wasan da za su tabbatar da makomar kulob din.

Tun da muna batu ne a kan kulob din Luneng, da fasaharsa ta horar da matasa kwallon kafa, babu yadda za a kammala wannan batu ba tare da tabo gasar cin kofin Weifang ba, wadda a kan gudanar a garin Weifang inda kulob din Luneng din yake. Gasar da makarantar Luneng take daukar nauyin gudanar da ita a ko wace shekara, wadda kuma ke kasancewa tamkar gasar Toulon da ake gudanarwa a kasar Faransa, wadda kuma take janyo hankalin fitattun 'yan wasa matasa na kasashe daban daban.

Bisa samun goyon baya daga hukumar kwallon kafa ta kasar Sin, da gwamnatin garin Weifang, makarantar wasan kwallon kafa ta Luneng ta gudanar da gasar cin kofin Weifang har karo 8, inda a ko wane karo a kan gayyaci 'yan wasan manyan kuloflikan kasa da kasa halartar gasar.

Ga misali a gasar da ta gudana a watan Yulin bana, an samu halartar wasu manyan kuloflika, kamarsu Wolfsburg na kasar Jamus, Sporting Lisbon na kasar Potugal, Sao Paulo na kasar Brazil, River Plate na kasar Argentina, da dai sauransu. Sakamakon taruwar kwararrun 'yan wasa matasa na kasashe daban daban a wannan gasa, ya sa dilallan 'yan wasan kwallon kafa su ma sun kan zo garin na Weifang, daga kusurwoyi daban daban na duniya, inda su kan yi bincike kan 'yan wasa matasa, tare da gayyatar wasunsu su zuwa buga kwallo a wasu fitattun kulofilika.

Game da dai wannan buri na sa na horar da 'yan wasa matasa, ban da shirya gasar cin kofin Weifang, kulob din Luneng shi ma ya kan tura masu horar da 'yan wasa zuwa ketare, domin su koyo fasahohin ci gaba, tare da samun karin ilimi. Wanda hakan ke daya daga matakan da kuloflikan kasashen Japan da Koriya ta Kudu suka taba dauka, wanda ya samarwa kasashen biyu kwaca-kwaca na zamani, bayan samun horo daga kasashen Brazil da Argentina, da dai sauransu.

Matakin da a kan dauka a da, ma'ana tura matashi guda zuwa ketare domin samun horo, wanda ke samar da mutum guda mai kwarewa, ya sha bam bam da na horas da koci fasahohi, domin da zarar ya komo gida, koci zai iya horar da matasa da yawa.

Bisa wannan hangen nesa ne Kulob din na Luneng ya kan tura masu horar da 'yan wasa zuwa Brazil da Portugal, inda sukan samu horo na fasahohi daga wasu manyan kuloflika, kamar su Sao Paulo da FC Porto. Haka kuma, ban da su masu horar da 'yan wasan, wadanda kulaf din ke turawa domin koyon fasaha a ketare sun hada da likotoci, da masu lura da harkokin yau da kullum na kolob din, gami da jami'ansa. Ta haka sannu a hankali, tsarin kulob din ke dada kyautata, ta yadda yake kara samar da fitattun 'yan wasa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China