in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara kyautata tsarin tattalin arziki a sabon yanayin da ake ciki
2015-03-11 16:48:06 cri

"Sabon tsarin yau da kullum game da tattalin arziki" kalma ce ba Sinawa ne suka kaddamar da ita ba. A gabar da ake fama da matsalolin tattalin arziki, dukkan muhimman kasashe na bin wani sabon tsarin yau da kullum game da tattalin arziki, wato kasancewar su su ma suna fuskantar matsalolin raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki, da raguwar guraban ayyukan yi, da rashin himmantu wajen samun ci gaba a gida.

Bisa wannan yanayin da ake ciki, kasashe daban daban na laluben sabbin fannonin dake iya inganta tattalin arzikinsu, ga misali: kasar Japan na neman sake farfado da tattalin arziki a kananan hukumomi, kasar Rasha kuwa na neman bunkasar sha'anin noma ne, sai kuma kasar Amurka wadda ke maida hankali ga hanyar bunkasar masana'antun kere-kere. Amma, a waje guda wasu kasashe na kokarin kyautata tsohon tsarin masana'antun su.

A nata bangaren, kasar Sin wadda ake kallo a matsayin injin bunkasar tattalin arzikin duniya, ita ma ta shiga sabon yanayin yau da kullum na musamman irin nata. Amma, sabanin sauran kasashe, kasar Sin tana fatan kara kyautata tsarin tattalin arzikinta a sabon zagaye, baya ga samar da tabbaci ga burin inganta tattalin arzikinta daga manyan fannoni.

Yayin da kasashe da dama ke samun tabarbarewar tattalin arziki sabanin halin da suke ciki a baya, kasar Sin ita da kanta ta zabi hanyar rage saurin bunkasuwa, da nufin neman kyautatuwar ingancin tukuna, a madadin neman yawan kayayyaki kawai.

Bisa wannan sabon yanayi na yau da kullum wanda ya jibanci tattalin arziki da duk duniya ke ciki, masana a fannin tattalin arziki na mayar da "gaggawa" da "bin son rai" a matsayin muhimman abubuwa dake taka rawa wajen samun nasara. Madam Chen Fengying, kwararriya a fannin tattalin arziki ta bayyana cewa,

"Sabon yanayin yau da kullum wani yanayi ne da ba a saba bi ba, wato ana cikin wani lokaci a gabar da ake fama da matsalolin tattalin arziki. Yanzu dukkan kasashe na kokarin kyautata tsarin tattalin arziki, da yin gyare-gyare kan tsarin masana'antu. Wadda take a gaba ce kadai za ta ci nasara."

A cikin rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin na sabuwar shekara, an tabbatar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya shiga sabon yanayin yau da kullum, lokacin da matsalolin da ake fuskanta game da tsare-tsare ke haifar da cikas ga bunkasuwarta. A ganin madam Chen, wadannan matsaloli sun shafi fannoni da dama. Chen ta ce,

"Mun samu matsaloli ne kan tsare-tsaren masana'antu, da na bunkasuwar yankuna, da na rarraba kudin shiga, da dai sauransu. Kuma mai yiwuwa ne daukar matakai uku a lokaci guda, za su zama muhimmin mataki na musamman a sabon yanayin yau da kullum."

"Kasancewar matakai guda uku a lokaci guda" a bakin madam Chen, hasashe ne da manyan shugabannin kasar Sin suka yi kan yanayin tattalin arziki da kasar ke ciki. Matakan guda uku sun hada da lokacin rage saurin bunkasuwa, da fuskantar mawuyacin hali akai-akai cikin gajeren lokaci, sakamakon kyautatuwar tsare-tsare, da kuma gudanar da manufofin inganta tattalin arziki sannu a hankali tun daga tushe.

Game da mawuyacin hali da za a rika fuskanta akai-akai, masani a fannin tattalin arziki na kasar Sin Jiang Yuechun yana mai cewa,

"Kyautata tsare-tsare na da wuyar gaske. Dole ne kasar Sin ta canja hanyar bunkasuwar tattalin arziki daga neman samar da kayyayyaki da yawa, zuwa neman ci gaba mai inganci, ta haka ne kawai za mu iya kara samun bunkasuwa yadda ya kamata a nan gaba."

Tun da kasar Sin za ta shiga mawuyacin hali sakamakon kyautatuwar tsare-tsare, ko cikin shekaru nawa za a iya kawar da wannan hali? Kwararru sun ba da jadawali na shekaru biyar. Game da hakan Madam Chen Fengying ta bayyana cewa,

"Mai yiwuwa ne a kawo karshen wannan sabon yanayi na yau da kullum kafin nan da shekarar 2020, wato cikin wa'adin lokacin gudanar da shirin shekaru 5 karo na 13. Baya ga wannan sabon yanayi na yau da kullum, za mu shiga wani yanayin bunkasuwa yadda ya kamata."

Tsawon lokaci da ake bukata wajen kyautata tsare-tsare ya dogara ne kan yanayin tattalin arziki da Sin ke ciki. A hakika akwai bambanci tsakanin yankuna daban daban wajen samun ci gaban tattalin arziki a nan kasar Sin. A ganin masana, bayan mawuyacin halin da ake ciki sakamakon kyautata tsare-tsare, kasar Sin za ta tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikinta na yau da kullum. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China