in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da cikakken zama na biyu na taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12
2015-03-09 10:12:46 cri

A jiya a yamma ne aka gudanar da cikakken zama na biyu na taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC karo na 12 a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, inda shugaban zaunennan kwamitin majalisar NPC Zhang Dejiang ya gabatar da rahoto a gun taron.

A cikin rahoton, Zhang Dejiang ya waiwayi manyan ayyukan da aka gudanar a shekarar da ya gabata a fannoni 7. Na farko, an bi jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin da tsarin majalisar NPC. Na biyu, an kara inganta dokokin kasar, da sanya dokoki su taka rawar bada jagoranci wajen gudanar da ayyuka. Na uku, a tsaida kuduri kan batutuwan shari'a bisa doka. Na hudu, a gudanar da aikin sa ido yadda ya kamata. Na biyar, a girmama muhimmin matsayi na wakilan jama'a, da inganta aikin wakilan na bada hidima ga jama'a. Na shida, a kara yin mu'amala tare da majalisun wakilan jama'a na larduna ko biranen kasar. Na bakwai, a kara gudanar da ayyukan yin mu'amala tare da kasashen waje da fadakarwa ta hanyar watsa labaru da dai sauransu.

Bisa bukatun zaunannen kwamitin majalisar NPC, mataimakin shugaban kwamitin Li Jianguo ya yi bayani game da daftarin gyarariyyar dokar tsara dokoki a fannoni shida, wato kyautata tsarin kafa dokoki, yin amfani da rawar jagorancin majalisar NPC yayin da ake tsara doka, sa kaimi ga tsara doka da zai dace da tsarin demokuradiyya, kyautata tsarin kafa dokokin gudanar da ayyukan gwamnati, kara duba takardun da aka adana don sake dubawa, da kuma takaita bayanin da aka yi game da dokoki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China