Za mu karfafa huldarmu tare da nahiyar Afrika, tare da maida hankali kan bukatun nahiyar domin bada kulawa ga wadannan fannoni uku, in ji mista Wang a yayin wani taron manema labarai da aka shirya a lokacin da ake gudanar da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC).
Faraministan kasar Sin Li Keqiang, a yayin ziyarar aiki da ya kai a nahiyar Afrika a shekarar bara, ya gabatar musammun ma da manyan ayyuka shida da kuma manyan hanyoyi uku na sufuri, wadanda kuma suka samu karbuwa sosai daga kasashen Afrika, in ji ministan. A watan da ya gabata, kasar Sin ta nada darektan farko kan wakilcin dindindin a kungiyar tarayyar Afrika AU, wani matakin da ke nuna a cewar mista Wang, goyon bayan kasar Sin game da dunkulewar Afrika.
Sin da nahiyar Afrika sun jima suna kasancewa cikin makoma guda. A shirye muke mu yi aiki tare da 'yan uwanmu na Afrika da canja dadaddar abokantaka tsakanin Sin da Afrika ta yadda za'a samu alheri da moriya tare, da kuma taimakawa kasashen nahiyar sauya albarkatunsu na cigaba zuwa wani hakikanin karfi na samun bunkasuwa, in ji mista Wang Yi. (Maman Ada)