Hakan a cewar ministan ma'aikatar cinikiayyar kasar Sin Gao Hucheng, na nufin kasar ta Sin, na da niyyar fadada hada-hadar shige da ficen hajojin cinikayya da kaso 6 bisa dari, kamar yadda firaministan kasar Li Keqiang ya bayyana, cikin rahoton ayyukan gwamnati, yayin zaman taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 da ya gudana a ranar Alhamis.
A cewar Mr. Gao wannan adadin ya gaza ci gaban kaso 7. 5, da a baya aka yi hasashen samu.
Kaza lika ministan cinikayyar ya ce a bana, yanayin harkokin cinikayyar gida da na waje bai yi armashi ba, don haka ake daukar matakan aiwatar da manufofi, wadanda za su kawo daidaito ga burin bunkasa matsayin cinikayyar kasashen waje.
Ya ce Sin za ta ci gaba da inganta harkokin cinikayya, da karfafa kasuwanci karkashin shirin bunkasa masana'antu, da daga matsayinta a hada-hadar kasa da kasa. Har wa yau za a kara maida hankali ga harkar inganta manufofin ci gaba ta hanyar bin sabbin dabaru, tare da nacewa fasahohin zamani na inganta harkokin cinikayya.
Bugu da kari minista Gao, ya ce Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayi na kasa da kasa, wanda zai baiwa 'yan kasauwar ta damar amfana daga hada-hadar fitar da kayayyaki. (Saminu Hassan)