
An bude taro na 2 na dukkan wakilan jama'ar kasar Sin a karkashin laimar zama na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC ta 12, a yau Lahadi 8 ga wata, a nan birnin Beijing. Inda a wajen taron, wakilan jama'ar kasar Sin fiye da dubu 2 suka saurari rahoton da shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC, mista Zhang Dejiang ya gabatar, dangane da ayyukan da zaunannen kwamitin ya yi a shekarar da ta gabata. Baya ga haka kuma, wakilan jama'ar kasar Sin za su saurari bayanin mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC, mista Li Jianguo, kan daftarin gyararren shirin dokar a fannin kafa dokoki.

Shugaban kasar Sin mista Xi Jinping, firaministan kasar Li Keqiang, gami da sauran manyan kusoshin kasar sun halarci taron.
An dai fara zama na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 12 ne a ranar 5 ga wata, kuma ana shirin kawo karshensa a ranar 15 ga wata.