Duk a wajen taron, jami'i mai kula da watsa labarai na gidan jakadancin kasar Cote D'Ivoire, Fieni Kouame, ya ce yana goyon bayan kasar Sin don ta tsara dokar a fannin dakile ta'addanci. Yana kuma fatan ganin kasar Sin a matsayin wata babbar kasa, za ta taimakawa kasashen Afirka a wannan fanni.
Tun yau wakilan jama'ar kasar Sin sun fara duba wasu tsare-tsaren gwamnatin kasar, gami da kokarin tsara wasu sabbin dokoki. Za kuma a kawo karshen zaman babban taron a ranar 15 ga wata, kamar yadda aka shirya.(Bello Wang)