Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce burin kasar Sin shi ne ta hada gwiwa tare da sauran kasashen duniya, wajen tabbatar da zaman lafiya da wadata mai dorewa a duniya.
Li Keqiang ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin. Ya ce kasar ta Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da samu nasara tare ta hanyar hadin gwiwa a cikin gida da waje, da aiwatar da manufar cimma moriyar juna, da tsayawa tsayin daka, kan tabbatar da moriyar samun ci gaban tsaron ikon mallakar kasar, da moriyar jama'a, da ma kamfanonin kasar dake kasashen waje da ikonsu bisa doka, da sa kaimi ga kafa sabuwar dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, bisa tushen hadin gwiwa da samun moriyar juna.
Ya ce ya kamata kasar Sin ta zurfafa yin shawarwari bisa manyan tsare-tsare, da hadin gwiwa a tsakaninta da manyan kasashen duniya, da nufin kafa tsarin raya dangantakarsu yadda ya kamata. A kuma ci gaba da yin kokari wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen dake makwabtaka da ita, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashe masu tasowa, da tabbatar da moriyarsu ta bai daya.
Har wa yau ya bayyana bukatar maida hankali kan harkokin kasa da kasa, da sa kaimi ga aiwatar da tsarin kasa da kasa bisa dokarsu yadda ya kamata. Sai kuma shiryawa da gudanar da ayyukan tunawa da cimma nasarar yakin Fascist, da yakin kin hare-haren sojojin Japan, kana da tabbatar da nasarorin da aka samu, da tabbatar da adalci bayan da aka cimma nasarar yakin. (Zainab)