in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tilas ne a aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje a sabon zagaye
2015-03-05 10:57:59 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana bude kofa ga kasashen waje a matsayin muhimmin aikin da ya shafi kwaskwarima da kasar Sin ke aiwatarwa.
A cikin rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin da ya gabatar, Mr. Li ya ce tilas ne a aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje a sabon zagaye, da gaggauta kafa sabon tsarin tattalin arziki, da yin takara a duniya ta hanyar bude kofa.

Ya ce ya kamata a sa kaimi ga kyautata tsarin cinikin waje, ciki har da kyautata tsarin mayar da harajin da ake karba kan kayan da aka fitarwa zuwa kasashen waje, kuma kwamitin tsakiya ne zai biya karin kudi da suka shafi hakan a sakamakon sabon tsarin, hakan dai za a iya samar da sauki ga kananan hukumomin yankunan kasa, da ma kamfanonin kasar.

Kaza lika ya bayyana alfanun kara yin amfani da jarin waje yadda ya kamata. Ciki har da gyara takardar ba da jagoranci ga 'yan kasuwa na kasashen waje game da zuba jari, da kara bude kofa a sha'anin ba da hidima da na kere-kere, da rage rabin yawan ayoyin kayyade 'yan kasuwa na ketare a fannin zuba jari a kasar Sin, da kuma gyara dokoki a wannan fanni, tare da kyautata tsarin sa ido don samar da yanayin cinikayya cikin adalci.

Firaministan ya ce akwai bukatar gaggauta aiwatar da manufar baiwa karin kamfanoni damar fita waje domin gudanar da harkokin cinikayya. A sa kaimi ga kamfanoni da su shiga hadin gwiwa wajen gina ayyukan more rayuwa a kasashen waje, da a fitar da na'urorin Sin na jiragen kasa, da na wutar lantarki, da sadarwa, da gine-gine, da kirar motoci, da jiragen sama da dai sauransu zuwa kasashen waje.

Ya ce a kafa sabon tsarin bude kofa ga kasashen waje, wato a sa kaimi ga kafa zirin tattalin arziki na siliki,da hanyar Silik ta ruwa ta karni na 21, da gaggauta gina hanyoyin zirga-zirga a fannin musayar kayayyaki a fadin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China