150305-Bello.m4a
|
Jakadan kasar Ghana dake kasar Sin, mista Anani Demuyakor, wanda ya halarci taron, ya ce rahoton da firaministan kasar Sin ya gabatar yana da kyau sosai, domin ya bayyana hakikanin yanayin da kasar Sin take ciki. Haka kuma a cewar jakadan Ghana, niyyar da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cin hanci da rashawa, gami da kokarin raya tattalin arzikinta a shekarar 2015, ta burge shi kwarai da gaske. Ban da haka kuma, ya ce karuwar tattalin arzikin kasar Sin, bisa matsayinta na wata babbar kasa mai babbar kasuwa, za ta amfanawa kasashen Afirka.