Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin na goyon bayan kokarin shimfida dimokuradiyya bisa doka a yankin Hongkong
A yau Litinin 2 ga watan Maris, mista Lv Xinhua, kakakin cikakken zama na shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya bayyana a nan Beijing, cewar game da batun yin gyare-gyare kan harkokin siyasa a yankin Hongkong, matsayin da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ke tsayawa a kullum a bayyane yake, wato gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta nuna goyon baya ga kokarin bunkasa tsarin dimokuradiyya a yankin Hongkong bisa doka a kai a kai, har zuwa lokacin da a cimma burin yin zabe tsakanin al'ummomin yankin gaba daya.
A yau da yamma ne aka shirya wani taron manema labaru game da cikakken zama na shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a nan Beijing, inda mista Lv Xinhua ya jaddada cewa, dole ne ka'idojin zaben gwamnan yankin Hongkong su dace da kundin tsarin mulkin yankin Hongkong da wasu bayanan da zaunannen kwamitin majalisar kafa dokokin kasar Sin ya yi, a yayin da suke dacewa da hakikanin halin da ake ciki a yankin Hongkong. Sannan, dole ne gwamnan yankin Hongkong ya kasance mai kishin kasar Sin da yankin Hongkong. (Sanusi Chen)