in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaf din Sporting ya doke Braga da ci 1 mai ban haushi
2015-01-15 14:41:58 cri
A wasannin mako na 16 na gasar kwallon kafar ajin kwararru ta Portugal, Sporting FC ya doke takwaransa na Braga da ci daya mai ban haushi a wasan da suka buga ranar Lahadi.

Dan wasan kasar Japan Tanaka ne dai ya ciwa Sporting din kwallo daya tilo, cikin mintuna goma na karshen wasan, bayan da ya canji dan wasan Colombia Fredy Montero.

Yanzu haka dai Sporting wadda ta samu nasarar wasannin ta 3 a jere, ta dare matsayi na 3 a teburin gasar ajin kwararrun Potugal da maki 33. Ya yin da ita kuma Braga ke matsayi na 5 da maki 28. Wannan ne kuma karon farko da Bragan ta rasa nasara a wasannin da ta buga a gida cikin kakar wasanni ta bana.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China