Ban da haka, za a kafa cibiyar manema labarai domin kula da harkokinsu, cibiyar da za ta fara aiki a ranar 27 ga wannan wata.
Manema labaran da suke son zuwa domin ba da labaran tarukan biyu dole ne sai su gabatar da bukatunsu. Manema labarai na kasashen waje da ke aiki a ofisoshinsu a nan kasar Sin ya kamata su gabatar da bukatun zuwa taruka biyu ga cibiyar manema labarai, a yayin da wadanda ke son zuwa kasar Sin cikin lokaci kadan domin tarukan biyu ya kamata su gabatar da bukatun ga ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashensu. Za a rufe karbar bukatunsu a ranar 25 ga wata.(Lubabatu)