in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Guinea ya yi kira da a yaki da kyamar addinin musulumci da kaifin kishin islama
2013-12-10 10:58:51 cri

A yayin bude taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar cigaban kasashe musulmi (OCI) karo na 40 da aka bude a ranar Litinin, shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya yi kira da yaki da kyamar addinin musulumci da kuma yaki da kaifin kishin islama, ta yadda za'a kafa zaman jituwa mai armashi a duniyar musulmi.

A cewarsa, duk da manyan cigaban da aka samu a shekarun baya baya, juyin juya halin da rikice-rikicen da ake samu a cikin wasu kasashen kungiyar OCI na kasancewa mahani dake janyo ja da baya wajen gina kasashen bisa tushen karko da zaman lafiya domin moriyar jama'ar musulmi baki daya.

Shugaban na Guinea ya yi kira da a samu hanyoyin warware tashe-tashen hankali da yake-yake, ta yadda za'a maido da zaman lafiyar al'umma da zaman jituwa tsakanin al'ummomin da suka yi fama da yake-yake.

Mista Conde ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka maido da zaman lafiya a kasar Mali tare da taimakon gamayyar kasa da kasa, da ma OCI, haka ma da kokarin da ake wajen maido da kwanciyar hankali a kasar Somaliya da kasashen Larabawa.

Haka zalika, shugaban kasar Guinea ya sake jaddada goyon bayansa ga kasar Palesdinu kan yaki da cin zarafi da danniya daga kasar Isra'ila dake cigaba da mamaye kasar Palesdinu, duk da amincewar da MDD ta yi wa Palesdinu a matsayin kasa.

An shirya taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar OCI bisa taken "Tattaunawa tsakanin al'ummomi, wata hanyar samun zaman lafiya da cigaba mai karko", taron zai mai da hankali kan matsalolin da ke hana cigaban kasashen musulmi tare kuma da karfafa zaman lafiya tsakanin kasashe mambobi na wannan kungiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China