in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mataulata na kasar Sin ya zarce miliyan 82
2014-10-14 16:32:40 cri
A halin yanzu, kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, amma duk da haka, akwai mutane da dama dake fama da matsalar talauci. A gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a ranar 14 ga wata, mataimakin shugaban ofishin kula da yaki da talauci na majalisar Zheng Wenkai ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata, mutane fiye da miliyan 600 da ke nan kasar Sin sun rabu da talauci, amma duk da wannan nasara, har yanzu akwai mutanen dake fama da matsalar talauci a kasar. Mr Zheng ya ce, bisa ma'aunin kasar Sin, akwai mataulata fiye da miliyan 82 a kasar a karshen shekarar 2013, amma bisa ma'aunin duniya, akwai mutane fiye da miliyan 200 dake fama da talauci a kasar.

Kasar Sin ta kebe ranar 17 ga watan Oktoba na bana a matsayin ranar farko ta kawar da talauci ta kasar, ana fatan za a kara jawo hankalin jama'a kan batun talauci. Bisa burin da aka gabatar a cikin rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin, an ce, kasar Sin za ta kara rage adadin da ya kai miliyan 10 na mataulata a kauyuka a shekarar bana. An ce, don cimma wannan buri, kasar Sin tana kokarin kafa tsarin kawar da talauci, da tsarin intanet game da abubuwan dake shafar aikin kawar da talauci, da taimakawa wajen kawar da talauci. Mr Zheng ya ce, za a gabatar da takardar jagorancin zaman al'ummar kasar da kawar da talauci a bana, da gudanar da ayyukan kawar da talauci ta hanyoyi daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China