in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kiran 'yan kasar Benin ga wata ranar yin adu'o'I domin zaman lafiya a ranar 11 ga watan Disamba
2014-11-16 17:02:35 cri
Hukumomin addinin kirista na kasar Benin sun gayyaci 'yan kasar, da kungiyoyin addinai daban daban da su kebe wata ranar yin adu'o'i domin kasar, a ranar 11 ga watan Disamba mai zuwa, a dukkan fadin kasar Benin domin kare zaman lafiya a cikin kasar, in ji wata sanarwar malaman addinin kiristan kasar Benin a ranar Asabar a birnin Cotonou.

Wannan kira an yi shi ne a yayin da rikicin al'umma a kasar Benin ya fara kamari tun cikin watan Satumba.

Jam'iyyun adawa, kungiyoyin kwadago da kungiyoyin fararen hula sun daga muryarsu domin bukatunsu da suka hada da ganin an tsaida ranar da ta dace ga zabubukan kasa. Musammun ma zabubukan kananan hukumomi da aka tsaida shiryawa kafin watan Disamban shekarar 2014, da kuma zabubukan 'yan majalisu da na shugaban kasar dukkansu a cikin watan Maris na shekarar 2015. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China