in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakokin da aka rera game da Ebola sun nishadantar da mutanen Afirka
2015-02-17 15:25:05 cri

Tun barkewar cutar Ebola a kasashen yammacin Afirka cikin watan Fabrairun shekarar da ta gabata, ya zuwa wannan lokaci mutane sama da dubu 20 ne aka tantance sun kamu da cutar, yayin da wasu mutane sama da dubu 8 suka rasa rayukansu bayan sun kamu da cutar.

Baya ga tsanantar da cutar ta yi a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, matakin da ya haifar da koma-baya ga tattalin arzikin kasashen da cutar ta shafa, a hannu guda cutar ta janyo damuwa tsakanin gamayyar kasa da kasa, dangane da harkokin kiwon lafiyar kasashen Afrika, da kuma kalubale ga samar da isashen abinci a nahiyar, ya kuma haddasa illa ga bunkasuwar harkokin al'adun da suka shafi wakoki a kasashen da cutar ta yi illa.

Sai dai duk da haka wakokin Afirka na ci gaba da samun bunkasuwa, bisa mataki na musamman, sun kuma nishadantar da jama'ar yankunan, da kuma cikakken bayani da Saminu Alhassan ya zai karanto:

A kasar Saliyo wadda ta fi fama da cutar Ebola, lokacin hutun 'yan kasar na kasancewa muhimmin lokaci ga makada wajen fitar da faya-fayai, amma a wannan karo kadan ne daga makada da mawaka suka samu wani abu daga harkokin nishadantarwa. Hasalima dai a cewar wani makadin kasar Jimmy B, yayin hutun shekarar da ta wuce, kusan harkokin rera wakoki sun kwanta a duk lokacin dari, babu wani ci gaba game da wannan harka ko kadan, ba a fitar da sabbin faya-fayai ba, kuma ba a gudanar da bukukuwan gabatar da wakoki ba, balle ma a samu kudaden raya fannin, sabo da babu wanda ke da niyar zuba jari cikin gonar da ba za ta yi yabanya ba.

A watan Yulin shekarar 2014, B Jimmy B ya taba bayyana cewa, zai yi taron rera wakoki a babban dakin wasan motsa jiki na kasar Saliyo, tare da gabatar da sabon faifansa. Amma sabo da umurnin hana taruwar mutane, da gwamnatin kasar ta fitar domin hana yaduwar cutar Ebola, dole Jimmy B ya canja lokacin gabatar da taron zuwa farkon shekarar 2015, inda ya kuma canja taken taron rera wakokin nasa zuwa "Ebola ba za ta hana wakoki ba", kana ya kuma gayyaci wasu shahararrun makada na kasarsa, da kasashen waje, domin shiga bikin da ya shirya, kafin daga bisani a sake soke taron bisa dai dalilin kaucewa yaduwar cutar Ebola.

A daya bangaren kuma wannan mawaki ya fuskanci koma baya a fannin yanayin zamantakewa ta hanyar fuskantar matsaloli da dama, musamman ma a fannin samun kudaden shiga.

Duk dai da cewa cutar Ebola ta haifar da illa matuka ga bunkasuwar harkokin wakoki, hakan bai hana yaduwar wakokin ba. A yanayin da ake ciki Jimmy B ya tsara wata waka mai suna "Ebola For Go", watau za a kawo karshen cutar Ebola, ya ce, yaduwar Ebola ta janyo mana tsoro da barazana irin wadda ba mu taba gani ba a baya, kuma kowa zai iya ganin hakan idan ya duba yanayin tattalin arzikin kasarmu, dukkammu muna fatan cutar Ebola za ta tafi cikin sauri, shi ya sa na fidda wannan waka "Ebola For Go" wadda ta yi babban tasiri ga jama'ar kasarmu, ta kuma kunshi yin kira ga jama'ar kasar da su dauki matakai yadda ya kamata, ta yadda za a iya samun nasarar hana yaduwar cutar cikin sauri.

A kasar Liberia kuma, da farko mutane da dama ba su amince da barkewar cutar Ebola ba, suna ganin cewa labarin bullar cutar wani shiri ne kawai na karya, da kuma makarkashiya da wasu kasashe suka tsara aiwatarwa.

Game da hakan, asusun yara na MDD ya gudanar da hadin gwiwa tare da wasu makadan kasar Liberia, inda suka kera waka mai taken "zuwan Ebola a gaskiya", domin yin kira ga jama'ar kasar, da su gane gaskiyar aukuwar annobar cutar, tare da daukar matakai cikin sauri na hana yaduwarta. Wakar ta bayyana cewa, "Ebola gaskiya ce, kuma ya kamata a kiyaye kai yadda ya kamata. Ebola gaskiya ce, ya kamata mu kiyaye iyalammu yadda ya kamata. Ebola gaskiya, ya kamata mu kiyaye kasarmu yadda ya kamata."

Mawakan sun yi amfani da salon waka mafi karbuwa a kasar wajen kera ta, ta yadda duk wanda ya ji ta sai ya sake rera ta. Aka kuma gabatar da ita ta kafar rediyo a dukkanin fadin kasar Liberia, matakin da ya sanya ta yadu cikin sauri, har ma wasu suka rika amfani da ita cikin wayar salula.

Kari mai dadin ji, da ganguna masu nishadantarwa, dukkansu sun kunshi muhimmin hali na al'adun Afirka, wanda ke daya daga cikin managarcin yanayi na zamantakewar jama'ar Afirka. Wanda duk da cewa ana fuskantar cutar Ebola, wakokin dake kunshe da wannan salo za su iya nuna karfin sihirinsu, su kwantar da hankulan jama'a, haka kuma su nishadantar, tare da sanya kyakkyawan fata a zukatan jama'ar nahiyar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China