in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar kalubale a fannoni da dama wajen kawar da cutar Ebola
2015-01-09 16:54:13 cri

A yayin da ake waiwayen yadda abubuwa suka wakkana a shekarar 2014, an gano cewa, cutar Ebola da har yanzu ke yaduwa a yammacin Afirka ta kasance wani abin da ba za a manta ba, a cikin shekara guda kawai, yawan mutanen da suka kamu sanadiyar da cutar ya wuce dubu 20. Za a iya kawar da cutar a cikin shekarar 2015 ko a'a? Gaskiyar maganar ita ce yankunan da suka fi fama da cutar har ma da kasashen duniya suna fuskantar kalubaloli da dama.

Tun bayan da aka fara gano cutar Ebola karon farko a shekarar 1976 har zuwa shekarar 2012, an samu barkewar cutar har sau 24 a wasu kasashen Afirka, ciki har da Kongo Kinshasa, Uganda, Sudan da dai sauransu, galibinsu a kauyuka ne masu nisa, kuma yawancin mutanen da suka kamu da cutar sun mutu cikin sauri, wannan ya sa cutar ba ta yadu zuwa sauran yankuna ba.

Amma, ya zuwa ranar 28 ga watan Disamba na shekarar 2014, yaduwar cutar Ebola da ta barka barke a wannan karo ya sanya mutane dubu 20 da 206 da aka tabbatar ko ake zaton sun kamu da cutar, yayin da mutane 7905 suka mutu.

A watan Agusta na shekarar 2014, hukumar kiwon lafiya ta WHO ta kaddamar da shirin magance cutar Ebola.I, inda aka bullo da matakan rage sabbin mutanen da za su kamu da cutar, da a yankunan da cutar ke yaduwa a cikin watanni 3, kana da hana yaduwar cutar a fadar gwamnati, da muhimman tashoshin jiragen ruwa, da sauran yankuna a cikin watanni 6 zuwa 9. Bisa shirin da aka yi, ana sa ran ganin za a kawar da cutar a watan Maris zuwa Yuni na bana.

Amma, a cewar Peter Piot, daya daga cikin wadanda suka gano cutar ta Ebola, kuma shugaban sashen nazarin kiwon lafiya na yankuna masu zafi na jami'ar London ya bayyana cewa, ko da yake an samu wasu ci gaba kan ayyukan yaki da cutar Ebola, amma duk da haka akwai yiwuwar cutar za ta ci gaba da yaduwa har zuwa karshen shekarar da muke ciki. Shi ma a nasa bangare, shugaban shirin tawagar musamman ta yaki da cutar Ebola na ta MDD mista Anthony Banbury ya bayyana cewa, watakila za a kawo karshen yaduwar cutar a karshen bana, amma zai yi wuya a cimma wannan buri a yanzu.

Yayin da yake ganawa da manema labaru, kakakin hukumar lafiya ta duniya WHO Tariq Jascha Ray Vecchi ya ce, abu mafi muhimmanci yanzu shi ne mu kara kokari, domin babu tabbaci kan yaushe ne za a kawo karshen yaduwar cutar.

Jascha Ray Vecchi ya kara da cewa, yanzu an samu raguwar yaduwar cutar ta Ebola. Ban da wannan kuma, tawagar yaki da cutar Ebola ta MDD ta gabatar da sabbin matakan binne gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar, da killace gaba dayan kebe mutanen da suka kamu da cutar kafin ranar 1 ga watan Janairu. A yanzu haka kasashen Guinee, Liberia da kuma Saliyo suna kokarin cimma wannan buri.

A fannin gwajin da aka yi kan allurar rigakafin cutar a asibitin, allurar da kamfanin harhada magunguna na GSK na kasar Burtaniya, da kasar Amurka suka ke nazari tare, ta tsallake gwajin farko.

Ko da yake an samu ci gaba sosai a wadannan fannoni, amma hakan ba ya nufin cewa, an kawo karshen yaduwar cutar. A makwanni uku da suka wuce, sabbin mutanen da suka kamu da cutar ta Ebola a kasashen Guinee, Liberia da Saliyo sun wuce 1400. Wannan ya sa wasu kwararru suke ganin cewa, bisa la'akari da yawan mutane da yankunan da cutar Ebola ta shafa, watakila cutar za ta ci gaba da kasancewa a yammacin Afirka na tsawon shekaru, kuma za ta ci gaba da yaduwa a wurin

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, bisa yanayin da ake ciki, ana bukatar kungiyoyin sa ido a kalla guda 10 da ke kunshe da mutane dubu 20 da za su kasance a muhimman yankunan da suka fi fama da cutar Ebola, don zakulo mutanen da suka kamu da cutar da ba a gano ba, da wadanda suka yi cudanya da su.

A nata bangaren, mai ba da taimako ga babbar daraktar hukumar WHO Mary Poller Gini ta bayyana cewa, idan ana son kawo karshen yaduwar cutar, kamata ya yi a kara kyautata tsarin kiwon lafiya da na aikin jinya. A ganinta, abin da ya fi muhimmanci shi ne, yammacin kasashen Afrikan nan uku su kafa tsarin aikin jinya da kiwon lafiya mai inganci, don magance duk wata barazana da za ta iyo kunno kai a nan gaba.

Kawo karshen yaduwar cutar Ebola, ba kawai ya shafi makomar jama'ar kasashen dake yammacin Afirka ba, har ma zai iya shafar harkokin kiwon lafiyan al'ummar duniya. Saboda haka, kamata ya yi hukumar WHO da kasashen duniya su ba da taimakonsu, domin ganin an hanzartar kawar da cutar ta Ebola a yankunan da ake fama ita. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China