in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitocin kasar Sin sun ba da gundummawa mai kyau wajen yaki da cutar Ebola a yammacin Afrika
2015-01-08 17:19:46 cri

Bayan barkewar cutar Ebola a yammacin Afrika a watan Fabrairun shekarar 2014 da ta gabata, gwamnatin kasar Sin, da sojojinta sun dauki matakan gaggawa, don baiwa kasashen yammacin Afrikan taimako har karo hudu. Tallafin da ya kai na kudin Sin miliyan 750. A sa'i daya kuma, ta tura rukunonin kwararru da likitoci kusan 10 zuwa wuraren da cutar tafi tsananta, yayin da masana a fannin yaki da cutar annoba, da masu aikin jiyya da Sin ta tura wuraren ya kai 1000.

Yayin bikin bada lambobin yabo ga ma'aikatan lafiya da suka yi fice wajen tallafawa al'ummun kasashen wajen na shekarar 2015, wanda ya gudana a ranar 6 ga watan nan, mataimakin shugaban sashin kula da hadin gwiwa da kasashen duniya, na ma'aikatar kiwon lafiya da kayyade iyali ta kasar Sin Wang Liji, ya yi tsokaci kan yadda likitocin kasar Sin suka tinkari kalubaloli, da mawuyacin hali, wajen bada taimako ga kasashen yammacin Afrika a fannin yaki da cutar Ebola, ya ce

"Tun barkewar cutar Ebola a kasar Guinea a watan Maris na shekarar bara, babu wani likitan kasar Sin dake cikin rukunonin aikin jiyya dake wadannan kasashen uku da cutar tafi yaduwa da ya nemi dawowa gida, suna ci gaba da aikinsu cikin tsawon lokaci, fiye da wa'adin da sauran mambobin da muka tura suka yi a baya. A Guinea, rukunin likitocin birnin Beijng da muka tura ya karbi wani mutum, wanda aka tabbatar ya kamu da cutar kwana guda da karbar sa."

Mr. Wang ya kuma bayyana cewa, an kare likitoci Sinawa biyu, da suka taba wannan mutum a sansanin rukunin don sa ido kan su, Allah ya taimake ba su kamu da cutar ba. Bayan sun fito, su ma sun ci gaba da aikinsu ba tare da bata lokaci ba har zuwa lokacin da aka maye gurbinsu. Ko da yake, ana fuskantar matsaloli da kalubaloli, rukunonin likitoci da Sin ta tura kasashen Guinea, da Laberiya da Saliyo, sun nace ga aikinsu na ba da taimako ga masu fama da rashin lafiya.

Diraktan ofishin kula da harkokin waje na sashin kiwon lafiya, a hukumar ba da hidima ta sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin Madam Li Rui ta ce, sojojin kasar Sin sun ba da taimako wajen gina wata cibiya, mai kunshe da gadoji 100 dake da na'urorin zamani, cikin wata daya a kasar ta Laberiya, tare kuma da tura wani rukunin likitocin soja 163, wadanda suka kware sosai kan aikin jiyya, dake gudanar da aikin yau da kullum a cibiyar. Sakamakon matsanancin halin da ake ciki, a wuraren da basu samu tallafin kayayyaki tun da farko ba, domin tabbatar da nasarar aikin ba da jiyya, likitocin soja na kasar Sin na fuskantar mawuyacin halin rayuwa ta yau da kullum, Madam Li ta ce

"Ba su da teburin cin abinci, yawancinsu a tsaye suke cin abinci, ciki hadda janar, da dukkanin sojoji da masu aikin jiyya, hakan ya burge ni sosai, amma wadannan wahalhalu ba su kawo cikas ga aikin na su ba ko kadan."

Wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO dake nan kasar Sin Dr. Bernhard Schwartlander, wanda ya halarci bikin, ya jinjinawa taimakon da kasar Sin ta bayar a wannan fanni. Yana mai cewa banda tsabar kudi da tallafin kayayyaki, Sin ta kuma taimakawa kasashen Afrika, wajen gina manyan ababen more rayuwa, da dakunan ayyukan gwaje-gwaje da sauransu. Ban da haka kuma, Sin ta tura fitattun likitocinta zuwa kasashen yammacin Afrika, dake fama da cutar don karfafa aikin da ake yi a yaki da cutar. Ya ce

"Wadannan masu aikin jiyya sun bar gidajensu, zuwa kasashen Afrika masu nisa, don ba da taimako wajen yaki da cutar Ebola. Matakin da ya shaida cewa, dukkansu fitattun jarumai ne, abin da ya kamata a baiwa muhimmanci shi ne, martaba wadannan mutane tare da mutunta su bisa jarumtakar da suka nuna."(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China