in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a kawar da cutar Ebola daga tushe
2014-12-30 16:20:13 cri

Cikin watan Fabarairun shekarar nan ta 2014 ne cutar "Ebola" mai saurin kisa ta bullo a kasar Guinea dake yammacin Afirka, ta kuma ci gaba da yaduwa cikin sauri a wasu kasashe, ciki har da Saliyo, da Liberia da dai sauransu cikin 'yan watanni. Sakamakon hakan ne kuma a watan Agustar da ya gabata, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ta bayyana wannan cuta a matsayin "Batun kiwon lafiyar na gaggawa".

Ya zuwa watan Disambar nan, cutar ta bulla a kasashe 8, da suka hada da Guinee, da Liberia, da Saliyo, da Amurka. Sauran su ne Mali, da Najeriya, da Senegal, da Spain. Yawan mutanen da ta kama kuwa ya kai kusan dubu 20, yayin da tuni wasu sama da 7,000 suka rasa rayukansu bayan kamuwa da cutar ta Ebola.

A wannan yanayin da ake ciki, akwai matukar bukatar magance sake yaduwar cutar, matakin da ya kasance babban kalubale a gaban kasashen duniya, musamman ma kasashen yammacin Afirka.

An dai bayyana wannan cuta ta Ebola a matsayin cuta da ta kasance mafi tsanani, tun bayan bullarta karon farko a shekarar 1976, kana yawan mutanen da suka kamu da ita, da wadanda suka mutu sakamakon cutar ya wuce jimilar da aka taba samu a tarihi.

Amma abun tambaya a nan shi ne, ko ta wane irin matakai za a iya dauka don magance wannan masifa da ake fuskanta a yanzu? Wasu na ganin akwai bukatar koyi daga dabarun da tarayyar Najeriya ta bi wajen kawar da cutar.

Idan dai ba a manta ba, a watan Yulin ne wani 'dan kasar Liberia mai dauke da cutar ta Ebola, ya isa birnin Lagos, birni mafi girma a Najeriya, matakin da ya haifar da bullar cutar karon farko a kasar.

A kuma gabar da ake nuna damuwa game da yiwuwar yaduwar cutar a wannan kasa mafi yawan jama'a a dukkanin nahiyar Afirka, an lura cewa Najeriyar ta cimma nasarar dakile yaduwar cuta, in ban da mutane 20 da suka kamu da cutar, ciki hadda mutane 8 da suka rasu sakamakon cutar.

Kafin daga bisani a watan Oktobar da ya gabata a sanar da kawo karshen cutar gaba daya a kasar. Game da hakan hukumar WHO ta ce, "hakan wata gagarumar nasara ce ta musamman da aka samu".

Game da fasahohin da Najeriyar ta bi wajen yaki da cutar Ebola, shehun malami kuma daraktan cibiyar kandagarki da shawo kan yaduwar cututtuka a Najeriya Abdulsalam Nasidi, ya bayyana cewa,

"ba tare da bata lokaci sun gane wannan kwayar cuta, da ta inda ta shigo Najeriya, daga nan muka fara bin sawunta, muka tabbatar da cewa mun shawo kanta, muka fitar da ita daga cikin jama'a don hana yaduwarta, yanzu muna shiryawa tsarin fadakar da mutanen kauyuka, da wadanda ba sa iya karatu su gani mene ne Ebola, yaya ake kawar da ita, inda za a yi amfani da yarukan Hausa, da Yarabanci, da yaron Igbo."

Bayan barkewar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afirka, wasu jami'an kiwon lafiya, da masu aikin jinya na kasashen da ta bulla sun fuskanci karuwar ayyuka, kuma kasancewar ba a iya daukar matakai masu amfani na kandagarki, da kuma rashin samun kudaden shiga yadda ya kamata, hakan sun sanya ma'aikatan jinya na wasu kasashe kauracewa aikin kula da masu dauke da cutar. Amma sai dai a Najeriya ba a samu irin wannan yanayi ba. Hakan kuwa na da nasaba da kokarin da gwamnatin kasar ta yi, tare da wasu manyan kamfanoni a aikin dakile yaduwar cutar tun daga tushe.

Alhaji Aliko Dangote shi ne mutum mafi arziki a daukacin nahiyar Afirka, kuma tun farkon bullar cutar ta Ebola, Attajirin ya shiga jerin masu bada tallafin jin kan jama'a, game da kandagarki, da kokarin dakile yaduwar cutar ta Ebola.

"mun yi kokarin a Najeriya muna daga cikin wadanda suka taimaka aka zo aka yi, za mu je dukkan filayen jiragen samanmu, za a sa injunan da idan ka zo wucewa idan kana da zazzabi zai iya dagawa ya nuna ka, don ganin cewa, ba mu kara samun wannan cuta ba.

Na biyu su raguwar kasashen yammaci mun ba da dala miliyan uku ga wannan abin da aka yi yau mu taimaka a kai.A na neman mutane dubu da za su je wannan kasashe guda uku,daga ciki mutane 520 daga Najeriya ne,To, ka san kowa ne lokaci Najeriya ta kan yi kokari ka san koda lokacin da suka samu yaki a Liberiya da saliyo,Najeriya ce kan gaba a wannan yaki.

Ban da kokarin da kasashen Afirka suka yi tare, an kuma bukaci taimako daga kasashen duniya. A kasar Saliyo wadda ta fi fama da cutar ta Ebola, akwai wata tawagar bincike, ta cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin, wadda ta bada gudummawa, har ma mataimakin daraktan cibiyar Gao Fu ya bayyana cewa,

"An riga an samu bullar cutar ta Ebola a Amurka da wasu kasashen Turai, kamar Faransa da kuma kasar Spain. Muna nan muna taimaka wa kasar Saliyo wajen yaki da cutar, a hakika muma muna taimakawa kanmu ne, kasancewar hana yaduwar cutar daga wadannan kasashen yammacin Afirka ya shafi dukkanin bangarori."

Bayan haka kuma, Gao Fu ya jaddada cewa, tawagarsa ba za ta bar kasar ta Saliyo ba, har sai an kai ga kawar da cutar baki daya daga kasar. Yanzu haka dakin gwaje-gwaje na tafi-da-gidan-ka, da wannan cibiya ta kafa ya fara samar da fa'ida. Gao Fu ya kara da cewa,

"Muna da wani babban shiri na taimakawa gwamnatin kasar Saliyo, wajen kyautata na'urorin kiwon lafiyar jama'a a nan gaba, wato za mu taimake ta wajen kafa wani dakin gwaji mai matsayin P3, ta yadda za a iya amfani da shi wajen ayyukan rigakafi, da na shawo kan wasu cututtuka." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China