in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka na fuskantar kalubale da damammaki a kokarinta na neman ci gaba
2015-02-03 16:44:52 cri

Bayan kammala taron shugabannin kungiyar kasashen Afirka AU karo na 24 a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha a kwanakin baya, wani bincike game da sakamakon da aka samu yayin taron, ya nuna cewa yankin dake kudu da hamadar Sahara, na fuskantar kalubale gami da damammaki, a kokarinsa na neman ci gaba.

Tun daga tsakiyar shekarun 1990, tattalin arzikin yankin Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke ta karuwa cikin sauri, lamarin da ya sanya yankin ya zama daya daga cikin yankuna mafiya saurin bunkasar tattalin arziki.

Bisa hasashen da Bankin Duniya ya yi, an ce a wannan shekara, karuwar tattalin arzikin yankin dake kudu da hamadar Sahara zai kai kashi 4.6%. Sai dai a daya bangaren, kimanin rubu'in yawan mutane masu fama da tsananin talauci a duniya, wato wadanda kudin gudanar da rayuwarsu a ko wace rana bai wuce dala 1.25 ba, suna zaune ne a wannan yanki na Afirka dake kudu da hamadar Sahara.

A cewar kwamishina mai kula da kayayyakin more rayuwa, da makamashi ta kwamitin kungiyar kasashen Afirka AU, Madam Elham Mahmoud Ahmed Ibrahim, yanzu haka manyan kalubalolin da kasashen Afirka suke fuskanta wajen raya tattalin arziki sun hada da neman samun ci gaba a bangarori daban daban, da sa kaimi ga aiwatar da gyare-gyare don daidaita wasu manyan tsare-tsare. Madam Elham ta kara da cewa, ya kamata a kara kwarin gwiwar kasashen Afirka, ta fuskar tinkarar kalubale a fannin hada-hadar kudi, da karfafa tushen masana'antu, da kara kokarin janyo zuba jari daga kasashen waje.

Alkaluman da aka samu daga Bankin Duniya sun shaida cewa, fiye da rabin mutanen da ke zaune a kudu da hamadar Sahara matasa ne 'yan kasa da shekaru 25, don haka al'ummun yankin da za su bukaci ayyukan yi a shekaru 10 masu zuwa, za su kai kimanin miliyan 11 a ko wace shekara. Sai dai alkaluma sun nuna cewa a halin da ake ciki, yawan guraben aikin yi da ake samarwa bai wuce rabin wadanda ake bukata ba.

A wani bangaren kuma yawan ma'aikata matasa da nahiyar ta Afirka ke samarwa, ya haifar da illa ga tattalin arzikin nahiyar, gami da damammaki na samun ci gaba. Kamar yadda wasu jami'an kungiyar AU suka bayyanawa wakilinmu, wasu kasashe ba su da wani cikakken tsari na masana'antu, wadanda za su iya sauya tsare-tsarensu na tattalin arziki.

A dayen bangaren kuma, Afirka tana da mutane da yawa, don haka ana maraba da masu zuba jari, wadanda za su iya tallafawa kokarin gina kamfanoni masu iya samar da guraben ayyukan yi da yawa, gami da masana'antu.

Ban da haka, a yayin taron kolin kungiyar AUn na wannan karo, an tsai da kudurin kafa wata cibiyar rigakafi, da shawo kan cututtuka, don tinkarar kalubalen da fannin kiwon lafiya ke fuskanta, gami da bazuwar annobar Ebola.

A nata bangare, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta fidda wani rahoto dangane da yanayin bazuwar cutar Ebola a ranar 29 ga watan Janairun da ya shude, inda ta ce tun daga karshen watan Yunin bara, yawan sabbin masu kamuwa da cutar Ebola, wadanda ake samu a ko wane mako ya yi kasa da mutum 100, alamar da ta shaida cewa bazuwar cutar ta kusan kaiwa karshe.

Dangane da hakan, mataimakin shugabar kwamitin kungiyar AU mista Erastus Mwencha, ya ce sannu a hankali, an fara shawo kan annobar Ebola, sai dai ba a kai lokacin da za a ce an kau da annobar baki daya ba tukuna. A cewar sa, yadda annobar take bazuwa ya nuna wasu matsalolin da kasashen dake yammacin Afirka suke fuskanta, kamarsu karancin zuba jari ga aikin kiwon lafiyar jama'a, da kasa daukar matakai cikin gaggawa, da dai makamantansu. Ya ce har yanzu kasashen dake fama da cutar Ebola suna ci gaba da fuskantar wasu manyan kalubaloli, da suka hada da rashin kayayyakin more rayuwa masu inganci, musamman a fannin kiwon lafiya, gami da karancin kudi.

A wani bangare na daban, mahalarta taron kolin kungiyar ta AU sun tabo batu game da yanayin da ake ciki na karuwar yawan kungiyoyin ta'addanci a nahiyar Afirka. An ce, yanzu haka a kalla akwai kungiyoyin 'yan ta'adda guda 16, da suke kokarin ta da zaune tsaye a kasashen Afirka, wadanda suka hada da 'yan Boko Haram, da dakarun al-Shabaab na kasar Somaliya. Bisa hakan ne kuma shugabar hukumar gudanarwar kungiyar AU, uwargida Nkosazana Dlamini Zuma, ta yi kira da a kafa wata rundunar kasa da kasa, wadda yawan sojojinta zai kai 7500, musamman ma domin dakile ayyukan 'yan Boko Haram.

Yayin wani taro da aka gudanar gabanin bude taron shugabannin kungiyar ta AU na wannan karo, Madam Zuma ta ce kokarin dakile dakarun Boko Haram, yana bukatar samun goyon baya mai karfi daga dukkan mambobin kungiyar.

A halin yanzu dai Najeriya da ta fi jin radadin ayyukan ta'addanci daga mayakan Boko Haram, da wasu kasashe 4 da ke makwabtaka da ita, wato Benin, da Kamaru, da Chadi, da Nijar, sun riga sun yarda su tura sojojin su don gudanar da hadin gwiwar kasa da kasa karkashin kungiyar ta AU, a wani mataki na ganin bayan kungiyar ta Boko Haram.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China