Gwamanatin Nigeriya ta ce, tana gudanar da wani shiri domin kara matakan tsaro a kan bakin haure a duk fadin kasar gabannin babban zaben dake tafe.
Kakakin ofishin shige da fice Chukwuemeka Obua ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya yi bayanin cewa, a yanzu haka an kwace katunan zabe na din din din guda 191 daga hannun 'yan kasashen waje a kokarin da ake yi na tabbatar da ba su shiga cikin zaben ba.
Wannan aiki ban da haka kuma ya gano katunan zabe na wucin gadi 57, tsaffin katunan shaidar 'yan kasa 367, da kuma wassu tsaffin katunan zaben 11 daga hannun 'yan kasashen waje, baya ga sabbin katunan shaidar kasa guda 68, takardun shaidan haihuwa 10 da takardun shaida na ofishin shige da ficen 3 duk a hannun bakin haure.
A cewar shi, wannan aikin da ake gudanarwa ya kai ga nasara kwato katunan haraji guda 6 na wata karamar hukuma da lasisin tukin mota 2 na wassu 'yan Nigeriya daga hannun bakin haure.
Har ila yau, an samu katin shaidar zama cikin barikin sojan Nigeria a hannun wani 'dan kasan wajen, takardar shaidar makarantar firamare da na shafin fasfo, in ji Mr Obua.
Duk wadannan kayayyakin, an same su ne a cikin jihohin Sokoto, Jigawa da kuma Zamfara. (Fatimah)