Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Suleiman Abba ya ja kunnen jami'ansa da su guji amfani da makamai a lokutan zabukan kasar da tafe,har sai hakan ya zama dole.
Babban sifeton ya yi wannan gargadi ne cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai bayan ya yiwa manyan jami'an 'yan sandan kasar da masu ruwa da tsaki jawabi a ofishinsa.
Ya ce, hakkin 'yan sanda ne su kare rayuka da dukiyoyin jama'a ba wai su kashe su ba, sabanin rahotanni da wasu kafofin watsa labarai ke watsa kan wannan batu.
Ya kuma ja kunnen jami'an nasa game da amfani da makamai barkatai da kuma illar da ke tattare ga take hakkin bil-adama kamar yadda hukumar kare hakkin bil-adama ta soke rundunar 'yan sandan cikin rahoton da ta fitar kan batun take hakkin bil-adama.
Suleiman Abba ya nanata kudurinsa na ganin jami'ansa sun martaba doka da kiyaye hakkin 'yan kasa, yana mai cewa, a shirye suke su samar da tsaro kafin da kuma bayan zabukan kasar.(Ibrahim)