Shugaban kasar Nigeriya Goodluck Jonathan a ranar Laraban nan ya musanta zargin taka rawa a takaddamar da aka yi wanda ya kawo jinkirta babban zabe, ganin yadda ake ta tsegumin shi ne sanadin dage zaben.
Zaben na shugaban kasar dai yanzu hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da matsar da shi zuwa nan da makonni 6, suna mai ba da dalilai da suka hada da tsaro, musamman ta bangaren hare haren Boko Haram.
Shawarar dage zaben, galibi masu suka game abubuwan dake gudana da ma babbar jam'iyyar adawar kasar suna zargin cewa, hakan ya nuna tsoron da jam'iyyar PDP mai mulki ke da shi na shankaye a zaben.
A cikin hirar shi ta kafar yada labaran talabijin din kasar na wata wata wato Media Chat a daren Laraban nan, Shugaban Jonathan, a cewar shi, ba'a tuntube shi ba kuma ba ya son a yi hakan saboda hukumar zaben mai zaman kanta ce kadai take da wannan iko bisa doka na matsar da zabe, don haka ita ta yanke wannan shawarar bayan ta tuntubi cibiyoyin tsaro da dama a kasar, yana mai tabbatar da cewar, daga shi har jam'iyya mai mulki ba su da hannu wajen jinkirta zaben.
A cewar shugaban kasar na Nigeriya, za'a rantsar da sabuwar gwamnatin demokradiya da aka zaba a ranar 29 ga watan Mayu a kasar. (Fatimah)