in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen Nigeriya ya yi gargadi da kalaman masu tunzuro rigima kan matsar da babban zaben kasar
2015-02-13 11:00:12 cri

Ministan harkokin wajen Nigeria Aminu Wali ya gargadi jami'an diplomasiyya a kan kalaman da za su iya tunzura rigima a kasar dake da masaukinsu game da harkokin cikin gidanta.

Wali ya yi wannan gargadin ne a wata ganawa tsakanin jami'an diplomasiyya a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, inda ya bayyana rashin jin dadinsa a kan ayyukan wadansu shugabannin ofisoshin doflomasiyyar wadanda suka saba wa ka'idojin aikinsu ta kafofin sadarwa.

Ministan ya ce, goyon bayan 'yan Nigeriya da ma 'yan kasashen waje, za'a gudanar da babban zaben kamar yadda aka tsara a bayan nan cikin kwanciyar hankali da lumana. Ministan harkokin wajen na Nigeriya daga nan sai ya ce, gwamnatin tarayyar kasar ta samu wadansu kalaman da abokan huldar 'yan Nigeriyan suka yi game da matsar da babban zaben a matsayin abin da bai dace ba ko kadan.

Ya ce, a bayyane yake karara cewar ba za'a iya gudanar da zabukan a jihohi uku ba dake arewa maso gabashin kasar kamar yadda aka shirya wato Adamawa, Yobe da Borno, kuma shawarar dage zaben kamar yadda shugaban hukumar zaben mai zaman kanta Farfesa Attahiru Jega ya sanar ya biyo bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki a wadannan wurare. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China