Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun yi maraba da dage zabukan Najeriya, tare da yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fagen siyasa da su girmama matakin hukumar zabe ta wannan kasa, in ji kwamitin kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS ) a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Kungiyar wannan shiyya ta bayyana cewa, ta yi maraba da wannan mataki na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na gusa zabukan kasar da aka tsai da shiryawa zaben shugaban kasa a ranar 14 ga watan Febarairu, har zuwa ranar 28 ga watan Maris, kana zaben gwamnoni da 'yan majalisun jahohi da aka tsai da shiryawa ranar 28 ga watan Febrairu aka dage su zuwa ranar 11 ga watan Afrilu, dalilin matsalolin tsaron da wannan kasa dake yammacin Afrika take fuskanta.
Duk da fahimtar damuwar mutane da karayar 'yan Najeriya da sauran jam'iyyun siyasa game da wannan dage zabukan, ECOWAS na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su amince da wannan mataki cikin gaskiya. Haka kuma shugabannin yammacin Afrika sun yi kira ga jami'an tsaron Najeriya da su yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankunan arewa maso gabashin kasar, inda kungiyar Boko Haram take nuna wuyar fatattaka. Kungiyar ECOWAS ta yi kira ga hukumar INEC da ta yi amfani da dage zabukan domin kammala dukkan ayyuka da shirye shiryen da suka jibanci zabukan masu zuwa, musammun ma batun rarraba katunan zabe na din din din, ta yadda za'a samu damar gudanar da zabuka cikin 'yanci da sahihanci.
A karshe, kungiyar ECOWAS ta jaddada muhimmancin girmama kundin tsarin mulki, tare da nuna goyon baya ga dukkan masu ruwa da tsaki wajen ganin sun kaucewa furta kalamai ko jawabai da za su iyar tura magoya bayansu tada fitina da tashe tashen hankali. (Maman Ada)