Wani babban jami'an sojan Najeriya ya bayyana cewa, Najeriya na amfani da wasu sabbin tsare-tsare da makamai a yakin da take da masu tayar da kayar baya a kasar.
Babban hafsan mayakan sama na kasar Air Marshal Adesola Amosun ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.
Don haka ya bukaci jama'a da kada su firgita da jin karar irin wadannan makamai daga lokaci zuwa lokaci. Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, wannan wata dama ce ta nazarin yanayin ruwan kasar domin kalubalen da ake fuskanta ba kawai a bangaren arewa maso gabashin kasar ba ne.
A cewarsa, shirin ya hada da sojojin sama, ruwa da kuma na kasa, kasancewar yaki da ta'adanci ba abu ne mai sauki ba duk da cewa, akwai sojoji na musamman da aka horas domin yaki da 'yan ta'adda.
Yanzu dai an kafa rundunar hadin gwiwa da ta kunshi dakarun kasashen Chadi, Nijar, Kamaru a kokarin da ake na ganin an kawar da 'yan ta'adda.(Ibrahim)