Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi alkawarin taimakawa Nigeria tunkarar hare hare na kungiyar Boko Haram da zimmar samun nasara a kan kungiyar.
Magatakardan MDD ya gabatar da wannan tabbaci ga Nigeria a cikin wani sako wanda wakilin shi na musamman a Afrika ta yamma Mohammed Ibn Chambas ya bayyana a lokacin da ya kai ziyara ga shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan a babban birnin kasar Abuja.
Magatakardan MDD ya kara da cewa, MDD ta baiwa Jonathan tabbacin cewar, za ta mara mashi baya a inda za'a maida hukumar kasa da kasa ta tabkin Chadi ta zamanto matattarar sojojin hadin gwiwa wadanda a yanzu ake kokarin hadawa domin yakar kungiyar Boko Haram.
Ban Ki-moon ya ce, MDD a karkashin bangaren samar da zaman lafiya za ta tabbatar da cewar, rundunar kiyaye zaman lafiyar ta Nigeria tana da cikakkken tsarin tafiyar da ayyukanta na tabbatar da cewar, ta murkushe kungiyar ta Boko Haram.
Magatakardan MDD ya ce, MDD za ta yi aiki tare da hukumomin Nigeria domin samar da taimakon agaji ga jama'ar da suka rasa muhallansu a jihohin da tashin hankalin ya shafa. (Suwaiba)