Dubannin jama'a mazauna garuruwan Bosso da Diffa sun tsere daga gidajensu bayan wasu munanan hare-hare na kwanaki 5 da kungiyar Boko Haram ta aiwatar a kan garuruwan.
Tun Juma'ar makon jiya ne garuruwan guda biyu dake jamhuriyar Nijar ke fuskantar munanan hare-hare daga kungiyar Boko Haram, wacce ke kaddamar da hare-harenta daga makwabciyar kasa ta Nigeria.
Duk da kasancewar rundunonin jami'an tsaro a garuruwan Bosso da Diffa, hakan bai kwantar da hankulan jama'a ba, domin kuwa dubun dubatar jama'a sai ci gaba suke yi da gujewa daga yankunan a cikin motoci kirar bas ko kuma kan mashin, wasu kuma suna dabar sayyada.
A yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin kasar Nijar, minstan harkokin waje Bazoum Mohammed ya ce, al'amarin yana kara rincabewa a garin Diffa inda mazauna garin ke arcewa daga garin sakamakon fargabar yiwuwar karin hare-hare daga 'yayan kungiyar tada zaune tsaye ta Boko Haram.
Ministan tsaro na Nijar Karidjo Mahamadou ya ce, an shiga halin kaka nika yi a Diffa, to amma ya ce, za'a dauki dukanin matakan da suka dace tare da taimakon sojoji da kungiyoyin agaji wajen tabbatar da cewa, an baiwa wadanda suka sulale kariyar tsaron lafiyarsu da kuma tabbatar da sun sami da kulawa ta abinci da wuraren kwana. (Suwaiba)