in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da bas dauke da fasinjoji 30 a arewacin Kamaru
2015-02-10 10:01:23 cri

Wata bas din fasinja mai dauke da mutane 30 ta fada hannun mayakan da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram a safiyar ranar Litinin din nan a garin Tourou, a arewacin Kamaru dake dab da kan iyaka da Nigeriya, kamar yadda wata majiyar tsaron soji ta tabbatar wa Xinhua.

Har yanzu dai ba'a san inda wadannan mutane da aka yi garkuwa da su suke ba, amma tabbas an yi musu kwantar bauna ne a kan hanyar da suke tafiya, in ji wannan majiya wadda ta kara bayanin cewa, ya zuwa yanzu dai sun tabbatar da cewa, motar na dauke da fasinjoji 30 lokacin da aka sace su.

Majiyar ta ce, a wani harin na daban da ya faru a ranar Lahadi, wassu sojojin kasar guda 9 sun ji rauni sakamakon arangama da 'yan kungiyar a garin Kerawa, shi ma a arewacin Kamaru, baya ga fasinjoji 11, 'yan kasar da aka kashe a cikin wata bas din a farkon shekaran nan a wannan yankin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China