Taron yaki da kungiyar Boko Haram zai kara fadada a nan gaba tare da duba yiyuwar da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen dake tsakiyar Afrika (ECCAS) take na tura sojojinta a yayin wani zaman taro a birnin Yaounde na kasar Kamaru, a wani matakin kawo goyon baya ga kasar Kamaru, mambar kungiyar shiyyar dake fama da ayyukan kungiyar Boko Haram ta Najeriya.
A gabanin wani taron gaggawa na shugabannin kasashe da gwamnatoci da aka tsai da yi ranar Litinin a birnin Yaounde, wani kuma zaman taron musammun na kwamitin tsaron kungiyar ECCAS na gudana tun daga ranar Alhamis zuwa Jumma'a a babban birnin na Kamaru, inda babban jigo guda na taron da ya shafi dabarun shiyyar domin yaki da kungiyar Boko Haram. (Maman Ada)