Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce, wani hari ta sama da kasa da dakarunta suka kaddamar sun yi nasarar murkushe wani harin da mayakan Boko Haram suka kai a garin Gombe da ke arewa maso gabashin kasar, inda suka gargadi jama'a da kada su fito zaben da za a yi a kasar a watan Maris.
Wani ganau mai suna Abu Hassan ya shaidawa manema labarai cewa, maharan sun fara kai hari garin Dadin Kowa ne, kimanin kilomita 40 daga birnin na Gombe, inda suka rika harbi da manyan makamai tare da tsorata jama'a.
Bayanai na cewa, harin da mayakan na Boko Haram suka kai garin na Gombe ya gurgunta harkokin saye da sayawa yayin da dakarun tsaro suka ci gaba da danna mayakan baya.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, mayakan dai na kokarin kafa sabbin sansanoni ne, bayan da aka fatattake su daga sansanoninsu da ke jihohin Adamawa, Borno da kuma jihar Yobe.(Ibrahim)