Mista Jega ya yi wannan furuci a yayin wani taron manema labarai, bayan tattaunawarsa da wasu manyan jami'an da abin ya shafa ta tsawon lokaci kan batun zabukan Najeriya. Ya ce, sabo da ci gaban hare-haren da Boko Haram suke kai a yankunan gabas maso arewacin kasar, sojojin kasar ba su iya tabbatar da tsaron kasar a yayin babban zaben ba, dalilin hakan, an yanke shawara cewa ya kamata a jinkirtar da lokacin babban zaben shugaban kasar, da kuma zaben gwamnonin jihohi da na 'yan majalisar dokokin kasar. Mista Jega na fatan za a iya tabbatar da tsaro a dukkan fadin kasar Nijeriya a yayin babban zabe.
Bisa ga abin da aka tsara a baya, an ce za'a gudanar da zaben shugaban kasar a ran 14 ga watan nan da muke ciki, a yayin da zaben gwamnoni jihohi da na 'yan majalisar dokoki a ran 28 ga watan, amma aka jinkirtar da lokacin zabukan bisa dalilan tsaro. (Maryam)