Hakan na da nufin dakatar kawar da kamuwa da cutar kwata kwata daga al'ummomin kasar baki daya, in ji ministan kiwon lafiya a cikin wata sanarwar da aka fitar albarkacin ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya da aka yi bikinta ranar 25 ga watan Afrilu.
Ministan kiwon lafiyan Afrika ta kudu ya yi amfani da wannan rana ta yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya domin mai da hankali kan cimma ayyuka, ci gaban da aka samu da matsalolin da ake fuskanta yayin dake yaki da wannan cuta a cikin kasar da ma wajen kasar, musammun ma a cikin shiyyar kungiyar SADC, in ji mista Popo Maja, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar.
Dalilin tsare tsaren kasa da na gundumomi na sanya ido kan cutar zazzabin cizon sauro, kasar Afrika ta Kudu ta samu nasarar rage cutar zazzabin cizon sauro a cikin kasar, tare da adadin masu dauke da kwayoyin cutar dubu 60 a shekarar 2000 zuwa matsakaicin adadin kimanin dubu 7 a kowace shekara.
Cutar zazzabin cizon sauro a Afrika ta Kudu na zuwa bisa yanayin lokaci kuma ta fi shafar yankunan kasar kamar Limpopo, Kwazulu-Natal da Mpumalanga. (Maman Ada)