A cewar wannan sanarwa, Alpha Conde ya isa kasar Afrika ta Kudu bisa gayyatar takwaransa na Afrika ta Kudu.
Tawagar gwamnatin Guinee na karkashin jagorancin shugaba Conde ta tashi daga birnin Conakry da sanyin safiyar ranar Jumma'a 23 ga watan zuwa Pretoria, babban birnin Afrika ta Kudu.
Bikin rantsar da shugaba Jacob Zuma, ya biyo bayan sake zabensa a matsayin shugaban kasar bisa wani sabon wa'adi na shekaru biyar.
A yayin zabubukan na ranar 7 ga watan Mayun da ta gabata, Jacob Zuma ya samu kashi 62,15 cikin 100 na kuri'un zabe tare da samun rinjayen yawan kujeru 249 cikin 400 na majalisar dokokin kasar. (Maman Ada)