Babban darektan hukumar kula da kamfanonin gwamnatin tarayyar Najeriya Benjamin Dikki ya ce, Nijeriya za ta dauki mataki na mai da bangaren sufurin kasar ya zamanto bangare mai zaman kansa.
Mr. Dikki ya ce, za'a fara kokarin tabbatar da hakan da za ran an kammala samar da doka da kuma tsarin da za'a bi na tabbatar da bangaren ya zamanto a hannun kamfanoni masu zaman kansu.
Wata sanarwa da Mr. Dikki ya raba wa manema labarai, ciki har da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ta ce, bangaren sufurin na Najeriya zai zamanto ya samu bunkasuwa kuma masu saka jari daga ko ina a duniya za su je Najeriya su saka jari.
Dikki ya ce, hukumarsa ta damu ainun da bangaren sufurin na Najeriya saboda muhimmancinsa a wajen bunkasar tattalin arziki kasar ta Najeriya, kuma shi ya sa suke kokarin ganin komi an yi shi bisa tsari na doka saboda kar a samu matsala kamar yadda aka samu matsala lokacin da aka yi kokarin kawo sabbin gyare-gyare a kan hukumar tashar jirgin ruwa ta Najeriya. (Suwaiba)