A kokarin da take na aiwatar da shirin raya sufuri, ta yadda za'a iyar kyautata jigilar kayayyaki da matakin bunkasa cigaban yankunan kasar, gwamnatin kasar Nijar ta dauki niyya a kwanan nan na zaben birnin Dosso dake yammacin kasar wajen kafa da amfani da tashar kasa ta farko a Nijar.
Gwamnatin kasar ta dauki niyyar aiwatar da wannan shiri a birnin Dosso da reshensa a birnin Yamai bisa kokarin habaka dangantakar harkokin kasuwanci tsakanin masana'antun gwamnati da masu zaman kansu.
Kamfanin harkar kudin kasa da kasa (SFI) shi ne aka rike a matsayin babban kwamiti da zai kula da wannan shirin domin ba da taimako ga tsara shi da kuma zaben wani 'dan kasuwa mai zaman kansa bisa kwarewarsa. (Maman Ada)