Kasashen Afrika sun yi alkawarin kafa wata dunkulaliyar kasuwar zirga-zirgar sufuri ta jirgin sama nan da shekara ta 2017.
Ministocin kasashen wadanda suka yi taro a Pretoria sun yi amana da shawarar da kwamitin hadin kan Afrika ta gabatar ga kasashen, inda hukumar ta bukaci kasashen na Afrika da su samar da wata kasuwar sufurin jirgin sama ta bai daya.
Ministar sufuri ta Africa ta Kudu Dipuo Peters ita ce ta zamanto mai masabkin taron na ministocin sufuri na Afrika CAMT, da kuma wasu ministoci 15 da aka zabo wadanda ke wakiltar ko wace shiyya ta Afrika dake karkashin kungiyar hadin kan Afrika.
Ministar sufurin ta Afrika ta Kudu Madam Peters ta bayyana cewar, ministocin na kasashen Afrika sun jinjinawa hukumar hadin kan Afrika saboda matakan da suke dauka na hankoron kafa kasuwar sufurin jirgin sama ta bai daya a Afrika.
Peters ta kara da cewar, samar da kasuwar sufuri ta bai daya, wani abu ne da zai hada kan kasashen dake nahiyar Afrika, tare da samun karin ingancin zirga-zirga jiragen sama da kuma kara bunkasa huldar tattalin arzikin da yawon buda ido da musayar al'adu a tsakanin kasashen Afrika. (Suwaiba)